Turai

Tsarin bayar da takardar Visa a Faransa

Faransa na shirin aiwatar da wani sabon tsari tareda tanttance adadin takardun shige da fice da muka sani da Bisa da ake baiwa jama’a musaman na kasashen dake jan kafa don mayar da nasu gida bayan da suka kasa cika sharuda na zama kasar.

Wasu daga cikin jami'an tsaro dake sa ido a wani shigen zige da fice.
Wasu daga cikin jami'an tsaro dake sa ido a wani shigen zige da fice. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Sakatary harakokin kasar ta Faransa dake kula da yankin Turai Clement Beaune ya ja kunen wadanan kasashe da cewa za su karfafa matakan zuwa wadanan kasashe mudin suka kasa daukar dawainiyar yan kasar don mayar da su gida.

Ya tunatar da manema labarai cewa a yayinda ministan cikin gidan kasar ta Faransa ya ziyarci wasu kasashen Larabawa, ya gabatarwa wasu daga cikin kasashen sunayen mutanen da ya dace a dawo da su gida.Faransa na daga cikin kasashen Turai dake neman kawo karshen zantukan da suka jibanci addini da kabilanci biyon bayan hare-haren da aka kai kasar a dan tsakanin nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI