Afrika

Yan adawa sun gindayawa Ouattara sharuda

Manyan jam’iyyun adawa a Ivory Coast sun gindayawa gwamnatin shugaba Alassan Ouattara sharudda kafin su amince da shirin tattaunawar sulhu don kawo karshen rikicin siyasar kasar na baya bayan nan da ya lakume rayukan mutane da dama.

Alassane Ouattara  da  Henri Konan Bédié a Otel du Golfe na Abidjan
Alassane Ouattara da Henri Konan Bédié a Otel du Golfe na Abidjan REUTERS/Luc Gnago
Talla

Daga cikin sharuddan da ‘yan adawar suka gindaya akwai soke dukkanin tuhume-tuhumen da ake yiwa jagororinsu da aka kame tare da sakin su, sai kuma janye jami’an tsaron da suka yiwa gidajen wasu jiga-jigan shugabannin ‘yan adawar kawanya.

A karshen watan Oktoba zaben Ivory Coast ya gudana, wanda hukumar zabe ta bayyana shugaba Ouattara a matsayin wanda ya yi nasarar lashe kashi 94 na kuri’un da aka kada.

Sai dai ‘yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben, tare da jagorantar boren bijirewa gwamnati, gami da shan alwashin yin gaban kansu wajen kafa gwamnatin rikon kwarya.

A makon da ya gabata ne shugaban kasar Alassane Ouattara ya gana da jagoran yan adawa,tsohon Shugaban kasar Henri Konan Bedie a Otel du Golfe na Abidjan,shugabanin biyu sun dau alkawali sake haduwa don duba wasu daga cikin zantuka dake hana ruwa gudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI