Da alama za a sallami kocin Super Eagles na Najeriya

Ministan matasa da bunkasa wasanni na Najeriya, Sunday Dare ya bayyana alamun yiwuwar sallamar kocin babban tawagar kwallon kafar kasar ta Super Eagles bayan wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika da Saliyo na ranar Talata.

Kocin Najeriya Gernot Rohr REUTERS/Heinz-Peter Bader
Kocin Najeriya Gernot Rohr REUTERS/Heinz-Peter Bader REUTERS/Heinz-Peter Bader
Talla

A haduwar da tawagogin 2 suka yi a ranar Juma’ar da ta gabata, Super Eagles na Najeriya sun yi sakaci har sai da ‘yan Saliyo suka farke kwallaye 4 da suka saka musu a raga.

Dare ya bayyana takaicinsa dangane da irin wannan rikitowa da Super Eagles suka yi, kana ya bukaci martani mai gauni daga gunsu a haduwar da za su yi a gobe Talata a birnin Freetown.

Sai dai ya ki cewa komai a game da dacewa ko rashin dacewar Gernot Rohr a matsayin kocin tawagar, inda yake cewa abin d ake gabansu shine samun tikitin zuwa gasar cin kofin Afrika.

Samun nasara a Saliyo zai bai wa Najeriya damar zuwa wannan gasa karo na 19.

Dare ya ce za su nazarci aikin Rohr don tantancewa ko shine ya dace ya ci gaba da horar da ‘yan wasan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI