Afrika

Kyakkiyawar hulda tsakanin kasashen Ecowas

Mama Sanni,Dan Majlisa a Jamhuriyar Benin
Mama Sanni,Dan Majlisa a Jamhuriyar Benin RFI Hausa

Kusan mako daya da Najeriya ta sanya hannu tareda amincewa da tsarin kasuwanci na bai daya da sauran kasashen Afrika, da dama daga cikin kasashe dake makwabtaka da Najeriya sun soma sa ran ganin an cimma matsaya ta gari.

Talla

Wasu daga cikin wakilan jama’a a zauren majalisar jamhuriyar Benin na fatan kula kyakkyawar hulda da takwarorinsu na sauran kasashe domin tabbatar da wannan buri.

Hakan ya sa yan Majalisu soma nazari don bullo da hanyoyin warware matsalar da ta sa Najeriya rufe kan iyakokin ta da wasu kasashen Ecowas.

Mama Sanni na daya daga cikin yan Majalisu a Jamhuriyar Benin ya bayyana fatan sa na kawo gaggarumar gudunmuwa don warware wasu daga cikin matsalolin .

Kyakkiyawar hulda tsakanin kasashen Ecowas

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.