Najeriya: 'Yan bindiga sun sace mutane 3 a kwalejin Nuhu Bamalli ta Kaduna

Misali na dan bindiga.
Misali na dan bindiga. The Guardian Nigeria

Wasu ‘yan bindiga sun sace mutane 3, kana suka harbe mutum guda bayan da suka kutsa gidajen ma’aikata na kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zaria a jihar Kaduna Najeriya.

Talla

Jaridun kasar su ruwaito cewa wani ma’aikacin kwalejin da baya so a bayyana sunansa ya ce da karfe 9 na daren Asabar ne ‘yan bindigar suka iso, kuma suka fara harbe harbe.

Shi ma da ya ke tabbatar da lamarin, shugaban kwalejin, Injiniya Kabir Abdullahi ya yi bayannin cewa lallai shugaban sashen tsaro na kwalejin ya kira shi ya shaida mai cewa ‘yan bindiga sun shiga rukuni gidajen ma’aikatan kwalejin, kuma sun yi awon gaba da Injiniya Bello Atiku, wanda shine shugaban sashen koyar da Komfuta.

Zalika, Injiniya Abdullahi ya kuma tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun harbi wani ma’aikacin kwalejin Sunusi Hassan a hannu  yayin da ya sha da kyar daga shiga hannunsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ASP Muhammed Jalige, ya suna bincike a kan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.