S.Sudan

Sama da mutane dubu 1 sun mutu a Sudan

Wasu daga cikin jami'an tsaron Sudan ta Kudu
Wasu daga cikin jami'an tsaron Sudan ta Kudu Alex McBride / AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, sama da mutane dubu 1 suka rasa rayukansu cikin watanni shida, yayin da aka sace akalla 400 sakamakon rikice-rikicen kabilanci a Sudan ta Kudu.

Talla

Har yanzu Sudan ta Kudu na kokarin murmurewa daga rikicin tsawon shekaru shida wanda ya tilasta wa gwamnati rarraba madafun iko a cikin watan Fabairu, matakin da ya kawo karshen tashin hankalin.

A baya-bayan nan dai, rikici ya tsananta tsakanin kabilu a kasar sakamakon dalilai mabanbanta da suka hada da barnar da shanu ke yi wa manoma.

Babban Jami’in Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Sudan ta Kudu, David Shearer ya ce, sama da mutane dubu 1 suka mutu a garin Warrap a cikin watanni shida kuma a yanzu haka akwai mutane da dama da suka yi azamar kaddamar da hare-haren fansa a cewarsa.

Jami’in ya gargadi cewa, wannan rikicin kabilancin ka iya kazancewa da zaran an shiga lokacin rani nan da watan Janairu.

A can kuwa gabashin Jonglei, daruruwan mutane ne suka mutu a rikicin, sannan fiye da 400 aka sace su, kuma akwai yiwuwar nan gaba kadan, tashin hankalin ya yi kamari a Jonglei a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Masu sanya ido sun gargadi cewa, rikicin kabilancin na yin barazana ga yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a cikin watan Satumban shekarar 2018 domin kawo karshen yakin da ya lakume rayuka kusan dubu 400 a kasar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.