Nijar

Hanyoyin kaucewa rikicin siyasa a zaben Nijar

Wata mata dauke da katin zabe a Jamhuriyar Nijar
Wata mata dauke da katin zabe a Jamhuriyar Nijar Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Yan kwanaki bayan da kotun fasalta kundin Tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar ta yi watsi da takarar madugun ‘yan adawa Hama Amadou dake neman shugabancin kasar a zaben dake tafe a ranar 27 ga watan Disamba, kungiyoyin farraren hula jama’a za su kaucewa tada rikicin zai jefa kasar cikin wani hali.

Talla

Kungiyoyin farraren hula a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da kira ga al’uma don ganin an kaucewa fadawa cikin rikicin siyasa a wannan lokaci da ake shirin shiga zabukan kasar.

Kiran kungiyoyin farraren hula na zuwa ne kwanaki hudu bayan da kotun fasalta kudin tsarin mulkin kasar ta fitar da sunayen yan takara a zaben shugabancin kasar na ranar 27 ga watan Disemba.

Yayin yanke hukuncin, shugaban kotun tsarin mulkin Bouba Mahamane ya ce, Hama Amadou dake takara karkashin jam’iyyar adawa ta ‘Moden Lumana’ bai cancanci tsayawa takara ba, saboda hukuncin daurin shekara daya a gidan kaso dake kansa.

Madugun adawar Hama Amadou wanda ya zo na biyu a zaben shugabancin kasar na shekarar 2016, ya fuskanci daurin shakara daya a gidan kaso saboda samunsa da laifin cinikin jarirai a 2017.

Sai dai ya samu afuwar shugaban kasa Mohamadou Issofou dangane da laifin da ya alakanta shi da siyasa.

A gefe guda kotun fasalta kundin tsarin mulkin ta amince da takarar Mohamed Bazoum dake neman shugabancin kasar karkashin jam’iyyar PNDS tarayya mai mulkin kasar, wanda wasu ke zargin ba cikekken dan Jamhuriyar Nijar bane.

Abdu Dan Neito daga kungiyar CODDAE a Jamhuriyar Nijar ya mana tsokaci a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.