Qatar zata karbi gasar cin kofin zakarun Kungiyoyin
Kasar Qatar zata karbi bakucin gasar cin kofin kungiyoyi da aka dage sabili da cutar Coronavirus a watan Fabrairun shekara mai kamawa kafin gasar cin kofin Duniya na shekara ta 2022.
Wallafawa ranar:
A watan Disemban shekarar bana ne ya dace a gudanar da gasar tsakanin zakarun kungiyoyi shida da za su kara tsakanin su da kuma kungiyoyin kasashen yankin a Doha.
A wannan sanarwa da Fifa ta fitar , hukumar ta bayyana cewa za a gudanar da gasar cin kofin kungiyoyi a karkashin hukumar Fifa ne daga ranar 1 zuwa 11 ga watan Fabrairun shekarar 2021.
Fifa tareda hadin gwiwar hukumomin kasar Qatar za su bayar da bayar kulawa don ganin an samu nasarar wannan gangami.
Indan aka yi tuni a shekara ta 2019 kungiyar Liverpool ce ta lashe kofin bayan da ta doke kungiyar Flamengo daga Brazil.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu