Duniya-Coronavirus

Tsawaita tattaunawa kan sayo allurar covid 19 na iya haifar da tsaiko

Shugaban kamfanin harhada magungunna da kimiya na kasar Amruka Moderna ya sanar da kasashen turai cewa tsawaita tattaunawa kan batun sayen allurar garkuwa cutar covid 19 na iya haifar da tsaiko wajen isar da maganin rigakafin,Duk da cewa akwai kasashen da aka fifita, wadanda suka saka hannun amincewa da sayen maganin tun cikin watanni da suka gabata.

Allurar garkuwar cutar Covid 19
Allurar garkuwar cutar Covid 19 Photo AP / Hans Pennink
Talla

Daga Cambridge a jihar Massachusetts, inda bafaranshen dan shekaru 48 da haihuwa da tun cikin shekara ta 2011 ke shugabantar kamfanin Moderna, dan karamin kamfanin da ya kirkiri maganin da yafi inganci wajen warkar da coronavirus, Stéphane Bancel, ya sanar da kamfanin dillancin labaren Faransa na AFP cewa, yanzu haka dai tattaunawa suke da Turai ba su tsaida ruwan miya ba kan cinikin maganin .

Kamfanin na Moderna da aka kafa a 2010 ya ce aikin gwajin allurar corona da ya samar ya cimma nasarar da ta kai ta kashi 95%, idan aka kwatanta da maganin da hadin guiwar manyan kamfanonin harhada magungunnan na kasar Amruka Pfizer da abokin kawancensa na kasar Jamus BionTech suka ce sun samar a makon da ya gabata.

Yanzu haka an dade ana tattaunawar tun ranar 24 ga watan Agustan da ya gabata tsakanin Moderna da kungiyar tarayyar turai kan sayen dozin miliyan 80 na allurar rigakafin, sai dai babu wata takamaimiyar magana da suka sakawa hannun tabbatar da ita a tsakaninsu

A halin da ake ciki yanzu, Moderna ya kulla yarjejeniyar ciniki da kasashen Canada, Japon, Israël, Qatar, da kuma kasar Britaniya. Baya ga dozin miliyan 100 da Amruka ta yi alkawalin saya tun cikin watan Agustan zuwa yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI