Najeriya

'Yan sandan Lagos sun yi arangama da 'yan acaba

Jami'an 'yan sandan jihar Lagos da ke kudancin Najeriya na ci gaba da arangama da masu sana'ar acaba, inda rahotanni ke cewa, rikicin ya kai ga harbe-harben bingida a babban birnin jihar, Ikeja a ranar Laraba.  

'Yan acaban Lagos na zargin jami'an 'yan sanda da cin zarafinsu tare da takura musu wajen neman abincinsu.
'Yan acaban Lagos na zargin jami'an 'yan sanda da cin zarafinsu tare da takura musu wajen neman abincinsu. REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Ko a jiya Talata sai da 'yan sandan na rundunar Task Force suka yi dauki-ba-dadi da 'yan acabar a kan hanyar Apapa da Oshodi, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar mutane da dama.

'Yan acaban sun yi ta kona tayoyi a tsakiyar manyan hanyoyi don nuna rashin amincewarsu da cin zarafin 'yan sanda a cewarsu.

Gaddafi Muhammad Yusuf, daya ne daga cikin masu sana'ar acaba a Lagos, ya shaida wa Sashen Hausa na RFI cewa, makasudin rikicin shi ne yadda 'yan sandan ke amfani da karfin da ya wuce kima wajen karbe baburansu.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren muryar Gaddafi wanda ya yi cikakken bayani kan yadda 'yan sanda ke sanadin ajalin 'yan acaba a Lagos.

'Yan sandan Lagos sun yi arangama da 'yan acaba

Gwamnatin Lagos ta haramta zirga-zirgar babura musamman a kan manyan hanyoyin jihar, amma masu sana'ar acaba na nuna turjiya suna cewa, ba su da wata hanyar samun abinci.

Sabon rikicin na zuwa ne a yayin da ake murmurewa daga barnar da zanga-zangar EndSARS ta yi wa jihar Lagos, inda fusatattun matasa suka lalata kadarorin gwamnati da kimarsu ta zarce Naira biliyan 400 a cewar hukumomi.

Zanga-zangar ta EndSARS ta samo asali ne biyo bayan korafi kan cin zalin da rundunar 'yan sandan da ke yaki da 'yan fashi ke yi wa jama'ar Najeriya, kuma tuni gwamnatin tarayya ta rusa wannan runduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI