Gambia ta doke Gabon- Caf na bukatar karin haske
Hukumar kwallon kafar kasar Gabon ta zargi Gambia da shirya manakinsa tareda dakatar da yan wasan kasar tsawon sa’o’i takwas a filin tashi dama saukar jiragen Banjul dake babban birnin kasar a jajuburin wasar da kungiyar ta Gabon za ta yi da Gambia dangane da gasar neman tikiti na shiga cin kofin nahiyar Afrika na Kamaru a shekara ta 2022.
Wallafawa ranar:

Yan wasan na Gabon da suka hada da Pierre Emerick Aubameyang sun share daren lahadi zuwa litinin da safe a filin tashi dama saukar jirage bisa dalili cewa hukumomin Gambia ba su kayakkin gwajin cutar Coronavirus.
An yi ta nuna hotunan yan wasa dake kwance a sarrarin filin tashi dama saukar jiragen Gambia.
Wasu na ganin cewa Gambia ta shirya haka ne don hana yan wasan Gabon kwana Otel, domin bayan share kusan sa’o’I takwas a wannan wuri, aka gunadar da wasa tsakanin kasashen biyu, Gambia ta yi nasara da ci 2 da 1.
Bayan koken hukumomin na Gabon ,hukumar kwallon kafar Afrika CAF ta bukaci a gudanar da bincike ,wanda hakan zai bata damar daukar matakan ladabtarwa ,har indan ta kama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu