Habasha - Tigray

Habasha na zargin Gyabresus da haddasa rikicin yankin Tigray

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus. Fabrice Coffrini/Pool via REUTERS

Rundunar sojin Habasha sun zargi Shugaban Hukumar Lafiya ta MDD, Tedros Adhanon Gyabresus wanda shine ke rike da mukafi mafi girma daga yankin Tigray da cewa shine kanwa uwar gami dake samarwa mayakan yankin nasa makamai da goyon bayan bijirewa Habasha da ya kaiga yakin da suke fafatawa yanzu haka.

Talla

Babban Hafsan sojan Habasha Berhanu Jula ya fadawa taron manema labarai a Addis Ababa cewa lallai suna da hujjoji dake tabbatar da cewa yayi shugaban na WHO yayi aiki tukuru don ganin Kungiyar fafatukan ‘yantar da alummar Tigray, wanda PM Abiy Ahmed ke cewa a yake su.

Yanzu haka yaki na ci gaba da ta’azzara a arewacin Habasha a yayin da a duk rana Sudan na karbar ‘yan gudun hijira dubu 3 da ke tsalaka kogin Tekeze, wanda ke iyaka da Sudan da Eritrea don su tsira da rayuwarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.