Taron samar da kudade ga kasashen yankin tsakiyar Afrika a Paris
Kungiyar kasashen tsakiyar Afrika CEMAC ta shirya taron samar da kudade da ya gudana a Paris, kungiyar ta samar da sama da bilyan uku a matsayin bashi daga hannun masu hannu da shuni.
Wallafawa ranar:
Akala bilyan 3 da dubu dari hudu na kudin Euros za a kara ga milyan 600 na wasu kudaden da aka samu a baya.
Kungiyar ta samu kusan bilyan 3 da dingo 4 na kudin euros a wannan taron samar da kudin zuwa yankin.
Yankin na daya daga cikin wuraren da ke da karancin masana’antu a Nahiyar Afrika, lamarin da ya janyo koma bayan gaske ta fuskar tattalin arziki da ma ci gaban yankin ga baki daya.
Kungiyar ta CEMAC na sa ran cimman wannan tsari na inganta yankin tareda bunkasa tattalin arzikin ta nan da shekara ta 2025, tsarin dake tattare da kusan shiri 84.
11 daga cikin wadanan shirye-shirye za a kashe kusan akalla bilyan 4 na kudin Euros a kan su.
Daga cikin manyan manufofin da kungiyar ta saka gaba, za a iya zana tsarin nan na inganta hanyoyin sufuri dake hada kasashen yankin, samar da isashen hasken wutar lantarki ga kasashen dake yankin tareda inganta hanyoyin sadarwa na zamani.
Kasashen na fatan warware wasu daga cikin matsalolin da suka shafi cinkoso da ake samu a tashoshin jiragen ruwa.
Wannan bashi dake a matsayin tallafi zai taimakawa kasashe shida dake yankin na Cemac da suka hada da Cameroun ,Congo, Gabon, Equatorial Guinee, Afrika ta Tsakiya da Chadi, kasashen dake fuskantar koma baya a fanoni daban –daban, inda alkaluma ke nuna ta yada yankin ya fuskanci koma baya da kusan kashi 17 cikin dari a maimakon kashi 40 cikin dari na yankin Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu