Afrika

Yan Sanda sun tarwatsa masu zanga a Kampala

Mutanen 3 sun rasa rayukansu a jiya laraba a birnin Kampala na kasar Uganda sakamakon wata mummunar arangamar da ta hada jami’an tsaro da masu zanga zangar dake cike da fushi, bayan sake kama dan adawar kasar Bobi Wine mawaki haka kuma dan majalisar dokoki, da ya kasance babban abokin hamayar shugaba Yoweri Museveni a zaben shugabancin kasar .

Mawaki, dan majalisa kuma dan takarar Uganda Bobi Wine
Mawaki, dan majalisa kuma dan takarar Uganda Bobi Wine France24
Talla

Yan sanda sun bayyana cewa sun kama dan adawar ne bayan da ya karya dokar corona ta hanyar gudanar da taron gangamin magoya bayanasa.

An sha tsare dan siyasar kuma mawaki Bobi Wine, sakinsa na baya bayan shine wanda aka yi ma sa a lokacin da ya halarci hukumar zaben kasar domin gabatar da takardunsa na takara a zaben shugabancin kasar na badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI