Afrika

Hukumomin karkara na taimakawa wajen rabon katunan zabe

A Jamhuriyar, hukumomin karkara na daga cikin masu taka gaggarumar rawa wajen fadakar da mutanen yankunan su domin a fito wajen karbar katunan zabe.

Wata mata dauke da katin zabe a Jamhuriyar Nijar
Wata mata dauke da katin zabe a Jamhuriyar Nijar Issouf Sanogo/AFP/Getty Images
Talla

Kusan mako daya kenan da hukumar zaben kasar ta soma raba katunan zabe ga al’uma.

Za a dai gudanar da zaben jamhuriyar Nijar ranar 27 ga watan Disemban shekarar bana.

Kungiyoyin farraren hula a kasar na ci gaba da kira ga jama’a da su kaucewa labaran karya da kan iya haifar da rikicin siyasa, kiran kungiyoyin na zuwa ne kusan mako daya bayan da kotun fasalta kudin tsarin mulkin kasar ta fitar da sunayen yan takara 30 daga cikin mutane 41 da suka shigar da takardun na neman tsayawa takara.

Adamou Amadou magajin garin Dan Tchandou a jamhuriyar ta Nijar ya bayyana mana cewa a wannan karon kamfanonin sadarwa na taimakawa a wannan rabon katunan zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI