Afrika

Komi ya kankama a zaben kasar Burkina Faso

Wasu daga cikin magoya bayan jam'iyyar  MPS a Ouagadougou na kasar Burkina Faso
Wasu daga cikin magoya bayan jam'iyyar MPS a Ouagadougou na kasar Burkina Faso RFI/Carine frenk

Yayinda suka rage kwanaki uku a gudanar da zaben kasar Burkina Faso,kungiyoyi masu zaman kan su na cigaba da bayyana damuwa ganin ta yada dubban mutane da suka baro gidajen su sabili da matsalar tsaro ba za su samun damar kada kuri’a ba.

Talla

Alkaluma na dada nuna cewa duban yan gudun hijira ne suka baro matsugunin su sabili da matsalar tsaro a arewacin kasar ta Burkina Faso.

Kungiyoyin masu zaman kan su sun shigar da kira ga hukumomin kasar na ganin su bullo da hanyoyi da suka dace don baiwa yan gudun hijira damar kada kuri’a.

Bangaren adawa,biyu daga cikin masu adawa da Shugaban kasar  kuma yan takara da suka hada da Zephirin Diabre da Eddie Komboïgo sun sha alwashin kawar da Shugaban kasar mai ci kuma dan takara Roch Marc Christian Kaboré daga karagar mulki.

Ali Sakola Jika mai sharhi kan lamuran da suka jibanci siyasar Burkina Faso ya bayyana irin manyan ayuka da sabuwar gwamnati zata mayar da hankali a kai.

Yau ne ranar karshe a yakin neman zaben da zai gudana ranar lahadi 22 ga watan Nuwamba shekarar 2020.

Komi ya kankama a zaben kasar Burkina Faso

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.