Faransa

Shugaba Macron ya karbi tawagar Musulman kasar

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci shugabannin Musulmai da su amince da "tsarin mulkin Jamhuriya" a wani tsari na yakar masu tsatsauran kishin addinin Islama a kasar.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Christian Hartmann/Illustration
Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya mika wannan bukata ne ranar Laraba,yayin da ya karbi bakwancin shugaban Majalisar koli ta Musulman Faransa (CFCM) Mohammed Moussa-oui da Chems-Eddine Hafiz, shugaban babban masallacin birnin Paris, da kuma wakilan gammayyar kungiyoyi 9 da suka kunshi majalisar ta CFCM din.

Tuni shugabannin na musulmai suka gabatar da Majalisar Limamai kamar yadda shugaba Macron ya bukace su, wanda zata dauki nauyin nada Limamai, da basu shaida ta gwamnati da kuma ka’aidojin tsarin mulki a karkashin tsarin jamhuriya.

Bin tafarkin jamhuriyar kamar yadda shugaba Macron ya bukata, na bukatar Musulunci a matsayin addini amma ba wata manufa ta siyasa ba, tare da haramta "katsalandan daga kasashen ketare".

Wannan matakin na a matsayin sabon tsari da zai kawo karshen limamai sama da 300 daga kasar yan asalin kasashen Turkiya da Morocco da kuma Algeria dake cikin kasar nan da shekaru 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI