An jera kwanaki 6 corona ba ta yi kisa a Najeriya ba
Alkalumma sun juna cewa babu wanda cutar coronavirus ta kashe a cikin kwanaki 6 na cikin makon da ya gabata, lamarin da ke nuni da cewa kasar na samun ci gaba da kwarewa a yakin da take da annobar.
Wallafawa ranar:
Hukumar da ke yaki da cututtuka a Najeriya ce ta sanar da haka, sai dai ba ta yi karin bayani a kan hanyoyin da take bi wajen yi wa masu fama da cutar magani ba.
Jimillar mutane uku ne suka mutu a fadin kasar a cikin kwanaki 8 da suka wuce sakamakon shake su da cutar ta yi.
Babu wanda cutar ta kashe ya zuwa ranar Juma’a, kuma mutane biyun da aka sanar sun mutu a ranar Alhamis, su ne na farko tun Juma’ar wancan makon.
Adadin wadanda cutar ta kashe a najeriya ya zuwa yanzu dai dubu 1 da dari da 65 ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu