Najeriya ta sake fadawa matsin tattalin arziki
Najeriya ta fada cikin matsin tatalin arziki a karo na biyu cikin shekaru 5 sakamakon annobar Covid 19 da faduwar farashin danyen mai, kamar yadda hukumar kididdiga ta kasar ta bayyana a ranar Asabar.
Wallafawa ranar:
Kudaden shigar kasar a rubu’i na 3 a wannan shekarar ya yi kasa a karo na 2 a jere, da kashi 3 da digo 62, a cewar hukumar kididdiga ta kasar.
Hukumar ta dora alhakin haka a kan faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya da kuma tasirin annobar coronavirus.
Kudaden shiga da ke da nasaba da danyen mai ya yi kasa da kusan kashi 14, idan aka kwatanta da kusan kashi 7 a rubu’i na 2, a cewar hukumar.
Asusun ba da lamuni na duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin kasar zai rikito da sama da kashi 5 a wannan shekarar, amma gwamnatin kasar ta ce zai fadi da kusan kashi 9.
Najeriya, wacce ita ta fi samar da danyen mai a nahiyar Afrika, kafin yanzu, tana samar da ganga miliyan 2 ne duk rana, amma tasirin annobar covid 19 ya sa ta sauka zuwa ganga miliyan 1 da dubu dari 4.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu