Kamaru

Wasu mata magoya bayan Kamto sun gudanar da zanga-zanga tsirara a Yaounde

Wasu 'yan kasar Kamaru yayin zanga-zangar neman sakin fursunonin siyasar kasar ciki har da Maurice Kamto a cibiyar Majalisar Dinkin Duniya dake New York
Wasu 'yan kasar Kamaru yayin zanga-zangar neman sakin fursunonin siyasar kasar ciki har da Maurice Kamto a cibiyar Majalisar Dinkin Duniya dake New York RFI Hausa

Rohatanni daga kasar Kamaru na cewa, jami’an tsaro a kasar sun kame wasu mata magoya bayan jam’iyyar adawa ta MRC da suka gudanar da zanga-zanga tsirara a birnin Yaounde, domin nuna adawa da ci gaba da tsare madugun ‘yan adawar kasar Maurice Kamto a gidansa.

Talla

Gomman matan wandanda akasarinsu masu yawan shekaru sunyi ta rera wakoki jinjin ga jigon adawar da kuma Allah wadai da matakin gwamnati na ci gaba da tsare shi, inda suka bukaci da a sake shi.

Wasu hotun zanga-zangar da aka watsa a kakafofin sada zumanta na Intanet, sun nuna wasu mata tsindir haihuwar uwarsu, suna tattaki a titunan Yaounde babban birnin kasar, kafin ‘yan sanda su tarwatsa su.

Yanzu haka madugun ‘yan adawar Maurice Kamto na ci gaba fuskanatar daurin talala a gidansa duk da cewa Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gaggauta sakin sa.

An yi wa Kamto daurin talala ne bayan ya kira wata zanga-zangar lumana ta nuna adawa da shugaba Paul Biya da ya shafe gomman shekaru yana mulkar Kamaru, yayin da Jami’an Kare Hakkin Bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya suka bukaci sakin sa tare da mukarrabansa da aka kama a ranar 22 ga watan Satumba.

Har yanzu jami’an ‘yan sanda da jandarmomi na ci gaba da zaman dirshen a kofar gidansa, kuma sun yi amfani da motarsu wajen toshe hanyar ficewa.

Sai dai sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta ce, matakin tsare Kamto ka iya zama take hakkinsa da kuma ‘yancinsa na gudanar da zanga-zangar lumana.

Lauyoyin Kamto sun ce, sun maka gwamnatin kasar a kotu domin kalubalantar matakin yi masa daurin talala, kuma nan kusa za a fara zaman sauraren shari’a a cewarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.