'Yan Burkina Faso za su yi zabe a yanayi na matsalar ta'addanci
A Lahadin nan al’ummar Burkina Faso za su kada kuri’a a zaben shugaban kasar a cikin yanayi na ta’azzara hare haren ‘ya ta’adda, zaben da ake kyautata zaton shugaba mai ci Roch Marc Christian Kabore zai samu galaba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sai dai ba za a yi zabe a kashi daya cikin 5 na kasar ba, inda akasarinsa ya fita daga ikon gwamnatin kasar, kuma yake fuskantar hare haren mayaka masu ikirarin jihadi kusan kullayaumin.
Tashin hankalin ya tilasta wa mutane miliyan 1 barin gidajensu, wanda ke a matsayin kashi 5 na yawan al’ummar kasar miliyan 20, kuma mutane dubu 1 da dari 2 sun mutu tun daga shekarar 2015.
Matsalar tsaron ce ta mamaye yakin neman zaben na gobe Lahadi, inda kuma aka aike da dakarun da ba a bayyana adadinsu ba don tabbatar da tsaro aranar zaben.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu