Har yanzu makwafta sun fi Najeriya tsadar fetur - NNPC
Duk da korafin da al’ummar kasar ke yi a game da tashin farashin albarkatun man fetur, gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu dai mai ya fi araha a kasar idan aka kwatanta da makwafta a yankin yammacin Afrika, kuma araharsa a kasar ke baiwa masu sumugal kwarin gwiwar ketarawa da shi kasashen waje.
Wallafawa ranar:
Wani babban jami’in gwamnatin kasar ya zake cewa arahar man fetur a Najeriya idan aka kwatanta da sauran kasashen da ke kewaye da ita ta sa harkar fasakaurinsa ke ci gaba da habaka.
Babban daraktan kamfanin mai, malakin Najeriya (NNPC), Mele Kyari, wanda ya bayyana haka a karshen mako ya ce kashi 80 na albarkatun man fetur da ake amfani da su a nahiyar yammacin Afrika daga Najeriya ake yin sumogal dinsu.
Ya ce akasarin kasashen yammacin Afrika ba sa sayen mai daga waje saboda rashin kudaden musaya na kasashen waje, saboda haka ya zama wajibi su dogara ga ‘yan sumogal daga Najeriya.
Mr Kyari ya ce gwamnatin Najeriya tana aiki wajen ganin ta halasta kasuwancin albarkatun mai da kasashen da ke kewaye da ita ta inda kasar za ta amfana.
Sai dai masu sharhi na ganin hakan wata hanya ce ta shaida wa ‘yan Najeriya cewa, farashin man fetur zai ci gaba da tashi, har sai ya cimma na sauran kasashen nahiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu