Najeriya

Kasa da kashi 10 na 'yan Najeriya ne ke samun ruwan fanfo - Rahoto

‘Yan Najeriya miliyan 18 ne kawai ke da ruwan famfo. Wannan adadi na wakiltar kasa da kashi 10 na ilahirin al’ummar kasar, a cewar wani sabon rahoto a kan ruwa da tsaftataccen muhalli da ake kira.

Misali an ruwan famfo.
Misali an ruwan famfo. © Milan Jeunesse
Talla

Bincike ya nuna cewa adadin ‘yan Najeriya da ke samun ruwan famfo mai tsafta ya sauka zuwa miliyan 18 a shekarar da ta gabata, daga miliyan 21 a wacce ta gabace ta. Sai dai babu tabbas ko adadin ya kara sauka a shekarar da muke ciki ta 2020.

Rahoton wanda aka wallafa a wannan wata ta Nuwamba, sakamakon bincike ne na shekara shekara da ma’aikatar albarkatun ruwa ta kasar tare da hadin gwiwar hukumar kididdiga ta kasar da UNICEF ke gudanarwa.

Wanna sabon rahoton shine na biyu a cikin binciken da aka tsara da zummar samar da amintattun bayanai da za su taimaka wajen tsara manufofi da kuma sa ido a bangaren samar da ruwan sha da tsaftacce a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI