Najeriya: Hari kan ayarin gwamnan Borno ya lakume rayuka 8

Majiyoyin tsaro a Najeriya sun ce adadin wadanda suka mutu sakamakon harin kwanton bauna da ‘yan ta’adda suka kai wa wani ayarin motocin sojin kasar, dake bada tsaro ga gwamnan jihar Borno ya kai 8, biyo bayan gano wasu karin gawarwaki biyu.

Dakarun sojin Najeriya.
Dakarun sojin Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa mutane shida da suka kunshi soji 5 ne suka mutu a harin, adadin da wata majiya ta dabam ta tabatar.

Mayakan kungiyar IS shiyyar yammacin Afrika, dauke da maanyan bindigogi da na’urorin harba rokoki ne suka bude wuta a kan ayarin motocin soji da mayakan sa kai a kauyen Kwayamti, mai nisan kilomita 60 dag Maiduguri, babban birnin jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Ayarin na kan hanyarsa ta zuwa garin Baga ne don samar da tsaro ga gwamna jihar Borno Baba Gana Umara Zulum wanda ya isa garin a jirgin sama mai saukar ungulu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI