Habasha-Tigray

Rikicin Habasha:A shirye mu ke mu kare Tigray da jininmu- Gabremichael

Firaminista Abiy Ahmed dai ya baiwa 'yan tawayen yankin wa'adin sa'o'i 72 don ajje makamai ko kuma fuskantar farmaki daga Soji.
Firaminista Abiy Ahmed dai ya baiwa 'yan tawayen yankin wa'adin sa'o'i 72 don ajje makamai ko kuma fuskantar farmaki daga Soji. Tiksa Negeri/Reuters

Shugaban Yankin Tigray da ke kasar Habasha Debretsion Gebremichael ya shaidawa Firaminista Abiy Ahmed cewar jama’ar sa a shirye su ke su mutu domin kare martabar yankinsu.

Talla

Cikin tsokacinsa kan kan wa’adin sa’oi 72 da Firaministan Abiy Ahmed ya basu na su aje makamai, Gebremichael ya zargi Abiy da kokarin rufa rufa kan irin illar da suka yiwa sojojin gwamnati.

Shugaban yankin ya ce Firaministan bai fahimci cewar su mutane ne masu kima da ke iya sadaukar da ran su domin kare yankin su ba.

Kalaman na Gebremichael na zuwa a dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasar ta Habasha wajen yin dukkan mai yiwuwa don bayar da cikakkiyar kariya ga fararen hular yankin na Tigray.

Tun a jiya Lahadi ne shugaba Abiy Ahmed ya gargadin dakarun da ke fafutukar ballewar yankin kan su ajje makamansu ko kuma su fuskanci luguden wuta daga Sojin kasar wadanda za su yiwa yankin Makelle mai jama'a dubu dari 5 kawanya don tabbatar da zaman lafiya.

Baya ga Majalisar Dinkin Duniyar dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam ciki har da Human Right Watch sun ja hankalin gwamnati wajen ganin ba a keta haddin fararen hula ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.