Kamaru

An tsaurara tsaro saboda zaben jihohi a Kamaru

Gwamnonin jihohin da ke fama da rikici a kasar Kamaru sun tabbatar da samar da tsaro yayin yakin neman zabe da ke gudana yanzu haka da kuma lokacin zaben na jihohi da zai gudana karon farko a ranar 6 ga watan Disamba.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya Ludovic MARIN / AFP
Talla

Gwamnan Arewa Mai Nisa dake fama da rikicin Boko Haram, Mijinyawa Bakary ya bayyana daukar wannan mataki yayin wani hira da yayi ta kafar radiyo da talabijin din kasar CRTV, inda yace hakan batun yake a yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin da ake amfani da turancin Ingilshi mai fama da rikicin 'yan aware.

Wasu jam'iyyun adawa ciki harda MRC ta jigon adawa Maurice Kamto sunyi kira da aka kauracewa zaben, sakamakon rashin mutunta wasu bukatu da suka mikawa gwamnati na gyara wasu dokokin zabe da kuma kawo karshen yakin 'yan aware kafin shirya zaben wanda shine karon farko da za'a gudanar da shi a kasar Kamaru.

Dangane da yakin nemam zaben, munji ta bakin Alhaji Muniru wani Kansila karkashin jam’iyyar UNDP mai adawa a Ngaundere dake arewacin kasar, wanda yace su dai a shirye suke don shiga zaben a dama da su.

Kuna iya latsa alamar sauti dake kasa don sauraron abin da Alhaji Muniru ke cewa;

An tsaurara matakan tsaro a yankunan Kamaru masu fama da riciki saboda zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI