Turai-Libya

Turai na shirin ladabtar da kassahen da ke ruruta rikicin Libya

Kafin yanzu dai Turai na zargin kasashen Rasha da Turkiya a matsayin wadanda suka hana ruwa gudu a kokarin kwantar da hankula a Libyan.
Kafin yanzu dai Turai na zargin kasashen Rasha da Turkiya a matsayin wadanda suka hana ruwa gudu a kokarin kwantar da hankula a Libyan. Getty Images

Kasashen Turai da ke kokarin kawo karshen rikicin Libya na barazanar daukar mataki kan duk wata kasa da ke zagon kasa ko kuma yunkurin kawo cikas ga yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla don warware rikicin Kasar.

Talla

Sanarwar hadin gwiwa da Kasashen Birtaniya, Faransa, Jamus da kuma Italiya suka fitar a litinin dinnan, ta bukaci al'ummar Libya da kuma sauran kasashe su janye daga duk wani yunkuri da zai kawo cikas ga kokarin da Majalisar Dinkin Duniya ke yi domin wanzar da zaman lafiya a Kasar.

Sanarwar ta kuma ce a shirye Turai ta ke ta dauki tsattsauran mataki a kan duk wanda aka samu da hannu wajen kawo cikas ga wannan shiri na wanzar da zaman lafiya a cikin kasar ta Libya, dama wadanda ke barnata dukiyar kasar da kuma masu take hakkin dan adam.

A can baya dai Turai ta zargi Rasha da Turkiyya da yin kutse a harkokin da suka shafi Libyan, saidai a wannan karo ba ta ambaci sunan kowacce kasa ba.

Kasashen yankin Turan hudu dai sun bayyana gamsuwarsu da tsarin da bangarorin Libyan suka fitar dangane da shirin zaben gama-gari da suka tsara yi a ranar 24 ga watan disamba mai zuwa, matakin da ke zuwa bayan kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a cikin watan Oktoban da ya shude.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.