Kotun Kamaru ta aike da lauyoyi 2 gidan yari kan barnata kayan gwamnati
Wallafawa ranar:
Wata Kotu a Kamaru ta daure wasu lauyoyi guda biyu watanni 6 a gidan yari, irin daurin jeka ka gyara halin ka, sakamakon samun su da laifin lalata kayan gwamnati da bijerewa gwamnati.
Me Claire Atangana-Bikouna, shugaban lauyoyin Kamaru ya ce lauyoyin biyu na kokarin karbar takardun shari’ar, domin ganin sun bar inda ake tsare da su.
An dai kama Richard Tamfu da Armel Tchuemegne ne ranar laraba a Doula, sakamakon arangamar da aka samu ranar 10 ga watan Nuwamba a kotu, inda 'yan Sanda suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa lauyoyin da ke zanga zanga domin ganin an saki wasu abokan aikin su.
Lauyoyi da dama sun samu raunuka a lokacin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu