Habasha - Tigray

Rikicin Habasha: Abiy Ahmed ya yi watsi da kiran kasashe kan yankin Tigray

Firaministan Habasha Abiy Ahmed.
Firaministan Habasha Abiy Ahmed. REUTERS/Tiksa Negeri

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed ya yi watsi katsalandan din kasashen duniya a harkokin cikin gidan kasarsa, sa’o’i kalilan gabanin cikar wa’adin da ya bai wa jagororin ‘yan tawayen Tigray su mika wuya, ko dandana kudarsu.

Talla

A Lahadi da ta gabata ne Firaminista Abiy Ahmed, wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a bara, ya bai wa ‘yan tawayen kungiyar Tigray People's Liberation Front sa’o’i 72 su mika wuya, amma shugabansu ya yi watsi da kiran, yana mai cewa al’ummar yankin da ke arewacin kasar a shirye suke su sadaukar da rayuwarsu don kare yankinsu.

A yayin da lokacin ke gabatowa, kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya gudanar da taronsa na farko a game da rikicin wanda aka shafe makwanni 3 ana yi, inda ya bayyana takaici a game da halin da fararen hula ke ciki a Makele, babban birnin yankin na Tigray.

Yanzu haka dai dakarun Sojin Habasha sun yiwa yankin na Tigray kawanya yayinad suka bukaci ficewar fararen hular da ke zaune a yankin.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi kashedin cewa hari a kan birnin zai zama laifin yaki, suna masu neman gwamnatin Habasha ta yi taka-tsan-tsan, don kaucewar asarar rayuka.

Sai dai Firaminista Abiy Ahmed ya yi watsi da kiran sasantawa, yayinda ya nanata cewa aikin tabbatar da doka a kan kungiyar TPLF ya shiga mataki na karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.