Faransa

Alkalai za su ci gaba da saurarar Sarkozy

Nicolas Sarkozy tsohon Shugaban kasar Faransa
Nicolas Sarkozy tsohon Shugaban kasar Faransa AFP

Za a ci gaba da shari’ar cin hanci da rashawa da ake tuhumar tsohon shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy a ranar Litinin mai zuwa, bayan da a yau Alhamis kotun hukunta laifuka ta yi watsi da bukatar a kori karar saboda dalilai na rashin lafiya na daya daga cikin wadanda ake tuhuma.

Talla

Likitocin da kotu ta baiwa umurnin tantance ikirarin rashin lafiyar daya daga cikin wadanda ake tuhumar,sun ce baya cikin hatsari, hasali ma zai iya bayyana a gaban kotu, lamarin da ya sa kotun ta yi watsi da bukatar dakatar da shari’a, maaimakon haka da dage zamanta zuwa Litinin mai zuwa.

Yayin gajeren zaman da aka yi a kotun, Niclas Sarkorzy, sanye da bakar rigar kwat sanye da Mayanin fuska ya nuna alamun hankalinsa a kwance yake, har ma da alama yana barkwanci da lawyoyinsa, yana kuma dan taba hira da manema labarai.

Sarkozy wanda ya dan daga wa siyasa kafa tun da ya sha kaye a zaben fid da gwani na jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya a shakarar 2016, amma kuma yana da tasiri a jam’iyyar ta Les Republicans, yana fuskanta daurin shekaru 10 a gidan kaso ko kuma tarar Yuro miliyan guda sakamakon tuhumar aikata rashawa.

Tsohon shugaban mai shekaru 65, ya musanta aikata ba daidai ba, kuma ya sha alwashin wanke kansa a gana kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.