Duniya

Al'umar Duniya kan iya dakile mace-macen da ake fuskanta

Wani asibiti dake kasar Birtaniya
Wani asibiti dake kasar Birtaniya

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi ikirarin cewa al‘umma ka iya dakile mace-macen mutane miliyan 5 da duniya ke gani kowacce shekara matukar aka rungumi wasu dabi’u musamman a halin da aka tsinci kai na annobar covid-19 da ta tilastawa jama’a zama a gida.

Talla

Cikin wasu dabarun sauya hali da kuma salon motsa jiki da WHO ta kaddamar jiya Alhamis ta ce idan har mutane za su mike tsaye tare kasancewa masu cikakken kuzari ko shakka babu yawan mace-macen da ake fuskanta zai iya zama tarihi.

Sabbin dabarun na hukumar lafiya kamar yadda hukumar ta sanar akwai bukatar motsa jiki ga dukkannin matas da dattijai naakalla mintuna 150 zuwa 300 kowanne mako ciki kuwa har da mutane da ke fama da matsananciyar rashin lafiya ko masu nakasa, yayinda hukumar ta kayyade motsa jikin mintuna 60 kowacce rana gay ara da matasa wanda ta ce da wadannan dabaru za a iya kawo karshen yawan mace-macen da duniya ke gani kowacce shekara.

Hukumar ta bayyana cewa bincikensu ya nuna cewa duk matashi 1 cikin sa’o’insa ko kuma magidanta 4 cikin 5 basa iya motsa jiki yadda yakamata a kowacce rana, wanda kuma ke haddasa cutukan da kowacce shekara ke lakume dala biliyan 54 don magance cutukan da hakan ke haddasawa, baya ga haddasa tafka asarar dala biliyan 14.

WHO cikin jawabin nata ta kuma karfafa gwiwar mata kansu rungumi dabi’ar motsa jiki hatta a lokacin goyon jiki ko shayarwa.

Haka zalika bayanan hukumar lafiyar ta duniya ya gargadi dattijai da su kaucewa yawan faduwa ko kuma buguwar bag aira babu dalili don tattalin lafiyarsu.

Hukumar ta WHO ta ce yawan motsa jikin ga kowanne rukunin mutane kama daga yara kanana matasa magidanta dattijai da kuma tsaffi na taimakawa wajen rage hadarin kamuwa da cutuka irinsu kansa hawan jini ciwon siga, yawan bacin rai da matsannacin tunani baya ga bugawar zuciya.

Kadan daga cikin amfanin motsa jikin kamar yadda WHO ta sanar na taimakawa matuka wajen kara kaifin kwakwalwa da kuma saukaka fahimta baya rage hadarin mutuwar far daya da mutuwar barin jiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.