Zimbabwe

Ana aikin ceto a Zimbabwe domin zakulo mutanen da kasa ta birne

Wasu daga cikin yankunan da ake hako zinari a Afrika
Wasu daga cikin yankunan da ake hako zinari a Afrika PHIL MOORE / AFP

Hukumomin Zimbabwe sun ce ana gudanar da aikin ceto bayan da wasu tarin ma’aikatan dake hakar ma’adinai suka makale a cikin rami sakamakon zabtarewar kasa a wani tsohon rami.

Talla

Jami’an gwamnatin kasar sun ce anyi nasarar zakulo akalla mutane 6 daga cikin sama da 20 dake cikin ramin.

Hakar ma’adinai ba tare da izini ba ya zama ruwan dare a sassan kasar sakamakon rashin aikin yi da kuma annobar korona.

Allah Ya wadata Zimbabwe da zinare da lu’u lu’u.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.