Najeriya

Arewacin Najeriya ne mafi hadarin rayuwa-Sarkin Musulmi

Fadar Sarkin Musulmi Sokoto
Fadar Sarkin Musulmi Sokoto

Sarkin Musulmin Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana cewar a wannan lokaci yankin arewacin kasar ne mafi muni wajen rayuwa sakamakon tabarbarewar tsaro a fadin kasar.Yayin da yake jawabi wajen taron Majalisar addini ta kasa, Abubakar ya koka kan tsadar rayuwa a cikin kasar, musamman abinda ya shafi kayan abinci da farashin sa yayi tashin goran zabbin da ya gagari talakawa da dama.

Talla

Sarkin Musulmin ya bukaci shugabanni da mabiyan su da su kyautata rayuwar su domin ta haka ne kawai za’a shawo kan matsalolin da suka addbi kasar.

Ya kuma bayyana matukar damuwa kan yadda Yan bindiga ke kai hari suna sace mutane har gidajen su, sabanin yadda suke yi a hanyoyi a shekarun baya.

Shugaban Majalisar Sarakunan yace ya zama wajibi jama’a su mutunta dokoki, musamman ganin yadda mutane suka yi ta zanga zangar adawa da wani sashe na Yan sanda inda yanzu haka wasu ke kokawa wajen ganin an dawo da su.

Sarkin Musulmin wanda ya yabawa jami’an Yan Sandan kasar saboda rawar da suke takawa, yace abin yi shine zakulo bata gari daga cikin su domin hukunta su, maimakon watsi da rundunar baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.