Wasanni

An gudanar da jana'izar Diego Maradona a Buenos Aires

Marigayi  Diego Maradona na kasar Argentiana
Marigayi Diego Maradona na kasar Argentiana Reuters

A yau ake gudanar da jana-izzar tsohon dan wasan marigayi Diego Armando Maradona a makabartar Buenos Airos kwana daya bayan mutuwar sa, a wannan wuri da aka sani lambun zaman lafiya ko jardin de la paix ,inda aka bine mahaifan sa.

Talla

Lauyan Diego Maradona a yau alhamis ya bayyana takaicin sa da rashin ko in kula daga direbobin motocin rashi lafiya da suka iso a makare wajen kai dauki ga marigayi Diego Maradona.

Lauyan ya bayyana cewa tsawon sa’o’I 12 aka samu wani jami’in kiwon lafiya da ya ziyarci mamaci,banda haka motar marar sa lafiya ta share kusan rabi aw aba tareda sun samu isowa bayan kiran da aka musu.

Lauyan mai suna Matias Moria ya bayyana bakin cikin sa,da kuma danganta mamacin a matsayin mutun mai hange nisa da ya rasu a jiya bayan fama da bugun zuciya ya na mai shekaru 60 a Duniya.

A India,ma'abuta kwallonkafa na ci gaba da bayyana alhinin su tareda bayyana cewa sun yi rashin abin bautar su wato Diego Maradona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.