Habasha

Gwamnatin Habasha ta yi shelar yaki kan yankin Tigray

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya umarci sojojin kasar da su kaddamar da farmakin karshe kan shugabannin yankin Tigray, yana mai cewa, wa’adin da aka ba su na mika wuya ya kawo karshe.

Sojojin Habasha sun yi damarar yaki da shugabannin yankin Tigray
Sojojin Habasha sun yi damarar yaki da shugabannin yankin Tigray REUTERS/Shabelle Media
Talla

Sanarwar da Firaminista Abiy ya fitar a shafin Twitter ta ce, yanzu haka an bai wa dakarun Hukumar Tsaron Habasha izinin kammala zango na uku kuma na karshe na kaddamar da farmaki kamar yadda dokar kasa ta bada dama.

Abiy wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a bara ya bai wa Kungiyar Tsagerun TPLF wa’adin sa’o’i 72 domin ajiye makamansu, yayin da shugabannin yankin na Tigray suka yi watsi da wannan wa’adi, inda kuma dakarunsu ke ci gaba da gwabza fada da sojojin gwamnatin Habasha, abin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, baya ga kimanin dubu 40 da suka rasa muhallansu.

Firaministan ya ce, dakarun kasar za su yi taka-tsan-tsan wajen kaddamar da farmakin don ganin ba a cutar da fararen hula ba, yana mai cewa, za a yi duk mai yiwuwa don ganin ba a lalata gine-ginen da ke birnin Makele ba da talakawa suka gina da jibin goshi.

Sai dai kawo yanzu babu cikakken bayani kan ko sojojin na Habasha sun yi wa birnin na Makele kawanya, yayin da aka gurgunta hanyoyin sadarwa a yankin na Tigray, sannan kuma aka takaita daukar rahoton abubuwan da ke wakana.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci shugabannin Habasha da su kare rayuwakan fararen hula, yayin da manyan kasashe da suka hada da Amurka ta Kungiyar Tarayyar Turai suka bukaci zaman sulhu karkashin jagorancin Kungiyar Tarayyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI