Hukumar lafiya ta zargi kasashen Afrika da gazawa wajen shirin samar da rigakafi
Hukumar Lafiya ta Duniya ta zargi kasashen Afirka da gazawa dangane da shirin samar da maganin rigakafin cutar korona wadda ke cigaba da dibar rayuka a kasahsen duniya. Ganin yadda aka samu akalla magunguna guda 3 da suka nuna sama da kahsi 70 na ingancin shawo kan cutar, Hukumar ta bukaci kasashen dake nahiyar da su tashi tsaye wajen shirya yadda za su yiwa jama’ar kasashen su allurar rigakafin.
Wallafawa ranar:
Sanarwar Hukumar ta bayyana cerwar ya zuwa yanzu kasha 33 ne kawai na kasashen dake Afirka ke shirin amfani da maganin daga cikin jerin kasashen duniya 40 da suka bayyana aniyar su na amfani da rigakafin.
Daraktar Hukumar dake kula da Afirka, Dr Matsidiso Moeti tace tsarawa da shirya yadda za’a yi aikin rigakafin shi zai tabbatar da nasarar sa.
Hukumar Lafiyar tace ana bukatar akalla Dala biliyan 5 da rabi wajen samarwa jama’ar Afirka maganin rigakafin, yayin da ake saran su amfana da maganin COVAX.
Bankin Duniya ya bada Dala miliyan 12 domin taimakawa kasashe matalauta wajen ganin sun amfana da maganin rigakafin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu