Najeriya

Manoman Najeriya na adawa da bude iyakokin kasar

Kan iyakar  Sèmè-Kraké tsakanin Najeriya da Nijar
Kan iyakar Sèmè-Kraké tsakanin Najeriya da Nijar RFI/Jean-Luc Aplogan

Yayin da Gwamnatin Najeriya ke shirin bude iyakokin kasar da ta rufe na dogon lokaci sakamakon dakile makamai da kuma haramtattun kayayyakin da ake shiga da su cikin kasar, wasu manoma sun bayyana rashin amincewar su da yunkurin gwamnatin.

Talla

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wasu daga cikin manoman na cewar bude iyakokin zai baiwa kasashen makota shiga domin sayen abincin da ake da shi, matakin da zai haifar da hauhawan farashi.

Ministar kudin kasar Zainaba Ahmed ta bayyana cewar nan bada dadewa ba gwamnati zata bude iyakokin sakamakon gamsuwa da matakan da aka dauka na dakile shiga da haramtattun kayayyaki cikin kasar.

Ahmed tace kwamitin da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa ya bada shawarar bude iyakokin, kuma yanzu haka yana nazarin rahotan da suka gabatar masa domin yanke hukunci a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.