Afrika

Kabore ya lashe zaben Burkina Faso

Shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré
Shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré LUDOVIC MARIN / POOL / AFP

Hukumar zabe  kasar Burkina Faso ta ayana shugaban kasar mai ci Roch Marc Chrstian Kabore a matsayin wanda ya lashe zaben kasar don zarcewa wa'adi na biyu.

Talla

Sanarwar da Hukumar zaben kasar ta bayar yau a birnin Ougadougou na kasar Burkina na  cewa Shugaba Roch Marc Christian Kabore yayi nasara a zagaye na farko da yawan kuri'u kashi 57,87%, kuma saboda haka ya sami zarcewa da Mulki waadi na biyu da yake nema.

Shugaban hukumar zaben Newton Ahmed Barry ya ce wanda yazo na biyu a zaben shine Eddie Komboigo dan takaran tsohon shugaba Blaise Compore wanda ya sami jimillan kuriu kasha 15.48% na jimillan kuriu da ake jefa.

A cewar Hukumar Zaben wanda yazo na uku shine Zephirin Diabre da ake dauka jagoran ‘yan adawa wanda ya sami jimillan kuriu kashi 12.46 % na yawan kuriun da aka jefa a kasar ta Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.