Bakonmu a Yau

An yi jana'izar tsohon Shugaban Nijar Tandja Mamadou

Mamadou Tandja, président ,tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar
Mamadou Tandja, président ,tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar (Photo : AFP)

Yau aka isar da gawar tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar Mamadou Tandja a Maine Soroa dake jihar Diffa, tsohon Shugaban wanda Allah ya yiwa rasuwa ya na da shekaru 82 a birnin Yamai.

Talla

Al’ummar kasar da dama na girmama tsohon shugaban saboda rawar da ya taka wajen gina ta da kuma dora ta a tirbar cigaban zamani.

To domin sanin irin rawar da tsohon Shugaban kasar Marigayi Tandja Mamadu ya taka ,Abdoulaye Issa ya tattauna da Mahamane Ousseini, tsohon Minista kuma daya daga cikin mutanen da suka yi aiki da marigayi. Jama'a da dama ne suka yi tattaki zuwa garin na Maine Soroa dake jihar Diffa domin halartar jana'izar tsohon Shugaban kasar Tandja Mamadou

Nijar ta rashin daya daga cikin masu kishin kasa,Tandja Mamadou

.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.