Najeriya

Ana bayan gida a bainar jama'a a kananan hukumomi 736 a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce kananan hukumomi 38 ne kacal suka yi nasarar magance matsalar yin bayan gida a bainar jama’a daga cikin kananan hukumomi 774 da ake da su a fadin kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Solacebase
Talla

Ministan kula da albarkatun ruwa Suleiman Adamu ya bayyana haka lokacin da ya ke kaddamar da shirin rungumar amfani da bayan daki wajen biyan bukata a fadin kasar.

Adamu ya ce yakin da suka kaddamar na ganin ana amfani da bayan gida ya samu nasara, inda kananan hukumomin da suka rungumi shirin wajen hana biyan bukata a bainar jama’a suka tashi daga 16 zuwa 38 a shekarar 2019.

Ministan ya ce yanzu haka wasu Karin kananan hukumomi 6 na kan hanyar samun irin wannan nasarar duk da matsalolin da kasar ta fuskanta bana na annobar korona.

Domin yabawa kananan hukumomin da suka samu nasara, ministan ya ce za’a fifita su wajen gabatar da ayyukan samar da ruwan sha na gwamnatin tarayya a cikin su.

Adamu ya bayyana damuwa kan yadda wasu jihohi suke kau da kai daga daukar matakin dakile wannan mummunar dabi’a wadda ke da matukar illa wajen kula da lafiyar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI