Najeriya

Ibrahim Abubakar Dan shekaru 50 ya kashe kansa ta hanyar rataya

Wani mutum Dan shekaru 50 ya kashe kansa ta hanyar rataya
Wani mutum Dan shekaru 50 ya kashe kansa ta hanyar rataya REUTERS/Morteza Nikoubazl

A jihar Kano, wani mutum mai suna Ibrahim Abubakar dan shekaru 50 ya kashe kansa ta hanyar rataya.Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe biyar na yammacin ranar Alhamis, a shagon sana’ar sa dake kan titin Zoo road, cikin birnin Kano a Tarrayar Najeriya.

Talla

A cewar makwabtan shagon marigayi Ibrahim, tare dashi suka gudanar da sallar la’asar, daga bisani kuma suka ji labarin rasuwar tasa bayan da wasu abokan kasuwancin sa suka an kara da halin da yake ciki a cikin shagon nasa.

Majiyoyi da dama dai sun tabbatar da cewar bashida wata lalurar damuwa ko tabin hankali, kafin rasuwar tasa.

Tuni dai rundunar yan sandan jihar ta Kano tace ta kaddamar da bincike kan lamarin, a cewar kakkakin ta DSP Abdullahi Kiyawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.