Najeriya

Kotu ta bada belin Sanata Ndume

Sanata Ali Ndume.
Sanata Ali Ndume. thisdaylive

Wata kotu a Abuja dake Najeriya ta bada belin Sanata Ali Ndume dake tsare a gidan yarin Kuje bayan ya kwashe kwanaki 5 sakamakon kasa gabatar da Abdurasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin fansho da ake zargi da almundahana.

Talla

Mai shari Okon Abang yace kotun tayi amfani da karfin ikon ta ne saboda dattakon da Sanata Ndume ya nuna lokacin da ake gudanar da shari’ar Mainan wanda ya tsaya masa a matsayin mai karbar beli.

Alkali Abang ne ya bukaci tura Sanatan zuwa gidan yari da kuma asarar gidan sa da ya kai miliyan 500 sakamakon gazawa wajen gabatar da wanda ya karbi belin sa a shari’ar da akeyi.

Sanata Ndume yace ya dauki matsayin tsayawa Maina ne saboda bukatar kotu na ganin an gabatar da mai rike da mukamin Sanata, kuma ganin ya fito daga mazabar sa ne ya say a gabatar da kan sa.

Tuni dai kotun ta soke belin da ta baiwa ‘dan Abdurasheed Maina, Faisal saboda kin gabatar da kan sa a gaban kotun lokacin da aka bukace shi.

Alkali Abang ya kuma bukaci jami’an tsaro su kama shi duk inda suka gan shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.