Najeria: Gwamnatin Kano ta fara aiwatar da tsarin ilimi dole

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. africatodaynewsonline

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan dokar bada ilimi kyauta kuma dole daga matakin Firamare zuwa sakandare a jiharBiyo bayan sanya hannu kan dokar, daga yanzu ya zama waji bi ga iyaye su sanya ‘ya yansu makaranta musamman wadanda suka kai munzalin soma karatuA lokacin da yake rattaba hannu kan dokar, Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce akwai hukunci mai tsanani ga duk iyayen da suka karya dokar a duk fadin jihar ta Kano.Daga Kanon ga rahoton Abubakar Isah Dandago