Faransa

An nuna wani bidiyon duka da yan Sanda suka yiwa bakar fata a Paris

Kylian Mbappé dan wasan Faransa dake taka leda a PSG
Kylian Mbappé dan wasan Faransa dake taka leda a PSG Susana Vera/Reuters

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafar Faransa mai taka leda a PSG Kylian Mbappe cikin juyayi ya bayyana bacin ran sa yan lokuta bayan da aka nuna wani bidiyo dake nuna ta yada wasu jami’an tsaro suka yi ta lakadawa wani mutun bakar fata duka a Paris.

Talla

Gwamnati ta sanar da dakatar da jami’an tsaron hudu biyo bayan yada wannan bidiyo.

Kylian Mbappe a wani sako ta twitter ya na mai cewa ya isa haka, a tsaida batun kyama, kazalika abokin wasar Mbappe Antoine Griezman ya na mai bayyana takaicin sa da cewa ya na mai bakin cikin yanayi ko halin da ake ciki a Faransa.

Gwamnatin kasar ta bayyana alhinin ta da kuma daukar alkawin magance irin wadanan matsaloli cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.