'Yan sanda Uganda za su yi bincike a kan kisan masu zanga zanga

Mawaki, dan majalisa kuma dan takarar Uganda Bobi Wine
Mawaki, dan majalisa kuma dan takarar Uganda Bobi Wine France24

Rundunar ‘yan sandan Uganda ta kaddamar da bincike a kan dirar mikiyar da jami’anta suka yi wa masu zanga zanga a makon da ya gabata , inda har mutane 45 suka mutu.

Talla

An kaddamar da binciken ne da zummar gano kurakuran da suka kai ga aika – aikar da ta yi sanadin rasa rayuka, kamar yadda aka jiyo kakakin rundunar ‘yan sandan na Uganda, Fred Enanga yana cewa.

Tuni manzannin kungiyar Tarayyar Turai suka yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa a game da matakan da ‘yan sanda suka dauka a kan masu zanga – zangar don tabbatar da an yi adalci ga wadanda abin ya shafa don kauce wa take doka a nan gaba.

A makon da ya gabata wasu mazauna yankin da aka gudanar da zanga zangar suka ce sun ga wasu jami’an tsaro sanye da kayan da ba na sarki ba, dauke da bindigogi yayin gangamin da masu zanga zanga suka yi don neman a saki dan takaran shugaban Uganda, Robert Kyagulanyi, wanda ake wa inkiya da Bobi Wine.

An tuhumi dan takaran jam’iyyar adawar da saba wa dokar takaita walwala da aka sanya don dakile annobar coronavirus, an kuma bayar da belinsa a yanzu.

A yau Juma’a, ministan tsaron kasar Janar Elly Tumwiine ya shaida wa manema labarai cewa jami’an tsaro na da damar bude wuta a duk inda masu zanga zanga suka wuce gona da iri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.