Turai

Zaman sauraran masu hannu a kisan Samuel Paty a Faransa

Shugaba Emmanuel Macron na karama Samuel Paty
Shugaba Emmanuel Macron na karama Samuel Paty François Mori/Pool via REUTERS

An gurfanar da wasu matasa hudu a Faransa da ake zargin su da hannu kan kisan malamin nan Samuel Paty, wanda wani dan Checenia dake gudun hijira a Farasar ya fille wa kai sakamakon nuna wa dalibansa zanen batanci ga addinin musulunci.

Talla

A farkon wannan watan, an tuhumi wasu kari dalibai 3 da hadin baki wajen file kan Samuel Paty a watan da ya gabata, biyo bayan nuna wa dalibansa zanen barkwancin da mujallar Charlie Hebdo ta yi na Annabi Mohammad, SAW, a matsayin wani bangare na darasin da yake koya musu a kan fadin albarkacin baki.

Kisan Paty ya janyo tada jijiyar wuya, lamarin da ya tilasta wa shugaba Emmanuel Macron yin dirar mikiya a kan masu tsatsauran ra’ayin Islamaa kasar da ke kokarin murmurewa daga radadin hare haren ‘yan ta’adda da suka lakume rayuka 250 tun daga shekarar 2015.

Uku daga cikin daliban da aaka gurfanar gaban kotu a ranar Alhamis, ana tuhumar su ne da nuna Paty ga makashinsa, Abdullakh Anzorov, mai shekaru 18, wanda ya fille wa kai a wata unguwa kusa da makarantar da yake koyarwa.

Wata majiya ta ce ana tuhumar daliban 3, wadanda shekarunsu 13 da 14 ne da laifin hadin baki a kisan ta’addanci.

Wacce ake zargi ta hudun, diya ce ga Brahim Chnina, mutumin da ya kaddamar da zazzafar gangamin yin tir da matakin Paty na nuna wa dalibansa zanen batanci ga Musulinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.