Afrika

11 ga watan Afrilun 2021 ne ranar zaben Shugaban kasar Benin

Patrice Talon Shugaban jamhuriyar Benin
Patrice Talon Shugaban jamhuriyar Benin Sia KAMBOU / AFP

Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta sanar da ranar 11 ga watan Afrilun shekarar 2021 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa.

Talla

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin shugaba Patrice Talon da musgunawa ‘yan adawa, inda har ya tasa keyar wasu daga cikin su zuwa kasashen ketare domin ci gaba da cin karensa babu babbaka.

A makon da ya gabat dai ne Shugaban kasar Patrice Talon ya kaddamar da ziyara zuwa jihohin kasar 12 da nufin jin koken mutanen kasar,yayinda wasu ke danganta wannan rangadi a matsayin yakin neman zabe.

Martabar Benin ta ragu a idon kasashen duniya bisa zargin gwamnatin kasar da mulkin kama-karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.