Afrika-Turai

Dukar bakar fata abin kunya ne a gare mu-Macron

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron Eric Gaillard/Pool via AP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce hotan bidiyon da aka nuna yadda jami’an Yan Sanda suka dinga dukar wani bakar fata ya basu kunya baki daya, yayin da aka tsare jami’an 4 domin fuskantar shari’a.

Talla

Macron ya bayyana matakin a matsayin abinda gwamnati ba zata amince da shi ba, yayin da ya bukaci jami’an sa da su bullo da tsarin da za’a yaki irin wannan mummunar dabi’a da nuna kyama saboda launin fatar bil adama.

Mutumin da aka yiwa duka a bidiyon Michel Zecler yace a lokacin da Yan Sandan ke dukar sa, suna kuma zagin sa saboda launin fatar jikin sa.

Wani da gidan sa ke kusa da wurin da aka ci zarafin Zicler, ya kuma nadi dukar a bidiyo, yace wani daga cikin Yan Sandan ya naushi Zickler akalla sau 7 a fuskar sa.

Yau asabar mazauna Faransa sun shirya zanga zangar adawa da dokar da ta hana daukar hotan Yan sanda lokacin da suke gudanar da aiki da yanzu haka ke gaban Majalisar dokoki.

Masu adawa da dokar sun ce matakin zai boye yadda jami’an Yan sanda ke cin zarafin jama’a da kuma kaucewa shaidun da za’ayi amfani da su wajen hukunta su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.