Wasanni

Kungiyar Al Ahly ta lashe kofin zakarun kungiyoyin Africa

Gasar cin kofin zakarun kungiyoyin Afrika a Masar
Gasar cin kofin zakarun kungiyoyin Afrika a Masar REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

Kungiyar Al Ahly ta kasar Masar ta lashe kofin zakarun kungiyoyi na Afrika bayan da ta doke a jiya juma’a kungiyar Zamalek da ci 2 da 1.

Talla

Wasar ta jiya ta hada kungiyoyin Masar biyu a filin wasa na Cairo ba tareda an baiwa yan kalo damar shiga sabili da cutar Corona Virus dake ci gaba da halaka rayukan jama’a.

Wanan dai ne karo na 9 da kungiyar ta Al Ahly ke lashe kofin zakarun Afrika,wanda zai kuma baiwa kungiyar damar wakiltar Afrika a gasar cin kofin Duniya na kungiyoyi da hukumar kwallon kafar Duniya Fifa ta shirya a watan Fabrairun shekarar 2021 a Doha na kasar Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.