Afrika

Mayakan Tigre sun cilla roka zuwa Asmara

Birnin Addis Ababa na kasar Habasha
Birnin Addis Ababa na kasar Habasha MIGUEL MEDINA/AFP

Kungiyar Kasashen Afrika ta Au ta aike da tawaga Addis Ababa da nufin ganawa da Firaministan Habasha Abiy Ahmed,a dai dai lokacin da aka cilla roka zuwa Asmara daga yankin Tigre.

Talla

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya gana da manzanin kungiyar kasashen Afrika ta AU a Addis Ababa, a wani hukunrin su na samar da mafita a yakin da ake tsakanin dakarun Habasha da na yankin Tigre.

Ganawar ta jiya juma'a na zuwa ne kusan kwana biyu bayan da Firaministan Habasha ya baiwa dakarun kasar umurni kai farmakin karshe zuwa yankin na Tigre.

Kasashen Duniya da kungiyoyi masu zaman kan su na ci gaba da bayyana damuwa tareda nuna alhinin musaman gani ta yada ake ci gaba da samun kwarrar yan gudun hijira farraren hula daga yankinna Makele dake da yawan al’uma kusan dubu 500.

Firaministan Habasha na ci gaba da yi kunen shegu ga duk wani kira daga kasashen waje,lamarin da yake kalo a matsayin kacan landan ga harakokin cikin gidan kasar ta Habasha.

A wata sanarwa daga fadar Firaministan Habasha,Abiy Ahmed ya na mai nuna godiyar sag a Shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa dake jagorantar kungiyar kasashen Afrika ta AU,da wakilan kungiyar da suka yi tattaki don taimakawa wajen warware rikicin yankin.

Firaministan Habasha ya bayyana cewa a hukumance nauyi ya rataya wuyan hukumomin kasar na dawo da doka da oda a fadin kasar,ya jima ya na mai kawar da ido a abinda ya kira tsokana daga mayakan Tigre,yayinda Ministan harakokin wajen kasar Habasha ya kaddamar da rangadi zuwa kasashe aminan Habasha da nufin kawo karin haske ga abinda wasu ke ganin cewa gwamnati na keta hakokin bil adam a yaki da dakarun Habasha ke yi da mayakan Tigre.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.